12 Mayu 2026 - 13:26
Source: ABNA24
Fashewar Bam A Pakistan Ya Kashe Da Raunata 25

Fashewar wani bam a jihar Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin Pakistan ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 7 tare da jikkata wasu 18.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, yayin da yake Allah wadai da wannan ta'addanci, ya bayyana cewa jami'an tsaro za su bi diddigin duk wanda ke da hannu a wannan mummunan hari har zuwa na ƙarshe, kuma za su hukunta su.

……………………………………………

Your Comment

You are replying to: .
captcha